Shugaban ‘yan sandan Mombasa Robert Kitur ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa a safiyar yau ne wasu ‘yan bindiga dadi suka bindige Mohammed Idris, shugaban kungiyar limamai da masu wa’azi na kasar Kenya a hanyarsa ta zuwa masallaci don ba da sallar asubahi.
Shi ma wani jami’in tsaron Mombasa ya ce maharan sun zo ne kan babur inda suka bude wa malamin wuta a cikinsa kana daga baya kuma ya cika a asibiti.
Ana zargin ‘yan kungiyoyi masu tsaurin ra’ayin addini ne suka bindige malamin saboda ya jima yana sukan irin ayyukan da suke gudanarwa a kasar Kenyan.ABNA